Der folgende Text stammt aus einem Klassiker der Hausa-Literatur, Magana Jari Ce ("Das Wort ist ein Kapital"), von Alhaji Abubakar Imam. In diesem dreibändigen Werk (entstanden 1937-39) findet man viele Themen und Motive aus nicht-afrikanischen Literaturen, u.a. auch aus europäischen Märchen. Das folgende Märchen ist eine Wiedergabe des Rattenfängers von Hameln.
Labarin Sarkin Busa
A wani gari can k'etaren Bahar Maliya a cikin k'asar Jamus, tun shekaru da yawa da suka wuce, Allah ya saukar musu da wani babbar bala'i. Aka saukar musu da b'eraye ko'ina cikin garin. B'erayen nan suka yi ta k'aruwa, har mutane suka rasa abin da su ke ciki, duk inda mutum ya duba garin ba ya ganin kome sai b'eraye. Ko wajen barci mutum in ya zo sai ya tarad da kamar ashirin tuk'u-tuk'u suna kwance. In hula ka ajiye, ko riga, kafin da safe sai ka tarar aljihun cike da b'eraye. In tak'aice maka labari, yawansu ba su k'idayuwa. In da za ka k'idaya su, ka k'idaya k'udajen da ke garin, sai ka ga sun fi yawan k'udajen nan kamar sau d'ari. Gari dai ba wajen sa k'afa, duk b'eraye ne.
Abinci kuwa mutum ko ya fi Aula dabara, ba yadda zai yi ya ajiye shi. Kome za a dafa sai a yi daidai da yadda za a iya cinyewa, don ko cikin akwati ka sa abinci ka kulle, sa san yadda za su yi wa akwatin nan huda, su shiga su cinye.
Duk wani abu da ka sani ana yi da fata sun cinye. Ba ka ganin mai takalmi, ko matashin kai, ko gafaka, ko buzu a garin. In ko sun kai ga abin da ba su ci, sai su yi masa hudoji, su bata shi. Ta ishe ka ma ko jariri suka tarar yana barci, sai su tasam masa da cizo za su cinye. Sai in ya yi kuka iyayen su k'wace shi.
In dare ya yi kuma su kan hana mutane barci da kuka da guje-guje. In sun ga jikin mutum waje, sai su kama da cizo, wai za su cinye shi. To, kada ka zargi mutanen garin, ka ga kamar sakarci ya hana su kasha su. Bala'i sai sa'ad da Mai abu ya sawwak'e abinsa. Da sun ga kare sai su tasam masa, su nuna masa Sarkin Yawa ya fi Sarkin k'arfi. Don kyanwa kuwa, wannan k'aramar alhaki, ba su kula da ita ba.
Abin mamaki, mutane kuma in sun tasam ma kashe su, sai ka ga kamar k'ara su su ke yi. Don a sa tarko kuwa, ko a sa dafi cikin abinci a ajiye, duk wannan ba ya rud'insu. Da sun gani sai su kewaye, kamar gaya musu a ke yi.
Duk mutanen gari suka rasa yadda za su yi, sai suka tasam ma mai garin, suna cewa shi ne ke da gashin tsiya, don tun da aka halicci duniya ba su tab'a jin irin wannan ba, sai cikin wannan zamani da ya ke sarauta. Suka ce ko dai ya san yadda zai yi da b'erayen nan, ko kuwa su fitad da shi, su kore shi daga k'asar.
Sarkin ya rasa inda zai sa kansa. Mutanen gari kuwa sai k'ara matsa masa lamba su ke yi. Ran nan yana zaune zugum, wad'annan dattijai su zo su zazzage shi su wuce, wad'annan su zo su zunzungure shi su wuce. Sai ga wani d'an tsoho bak'o ya zo, ya duk'a ya gai da Sarki.
Sarki ya dube shi, ya gan shi wani iri, sai ya ce, "Malam, daga ina? Wace sana'a ka ke yi?"
Tsoho ya ce, "Ga ni dai. Inda na fita da nisa, amma sana'ata busa, har mutane na kirana Sarkin Busa."
Sarki ya ce, "To, sai ka je ka sauka, in kana iya sauka nan, mu ba ta busa mu ke yi ba yanzu, ta kawunammu mu ke yi da wannan bala'i."
Sarkin Busa ya ce, "Ai ni ma ba busar banza na ke yi ba, wani asiri Allah ya ba ni wanda in na yi busa duk ko wane abu mai rai ya biyo ni. Da kwad'i, da macizai, da b'eraye, da dukan naman ruwa da na tudu, da tsuntsaye, har da masu tafiya da kafa biyu, duk wanda ya ji na yi busa, ba sauran zama, sai ya yi ta bi na. Don wad'annan 'yan b'erayen da suka dame ku, in ka iya ba ni abin da na ce, yanzu sai in raba ku da su?"
Sarkin ya ce, "Don Allah, ka taimake mu! Kome ka ke so nan duniya na ba ka. Tambayi, mu ji."
Sarkin Busa ya ce, "Ka ba ni sule d'ari, in na raba ku da su?"
Sarkin ya dube shi, ya ce, "Yau ga abin mamaki, mene ne sule d'ari kuma! Sule dubu goma ma, in kana so sai in ba ka. Kai dai mu rabu da wannan bala'i."
Sarkin Busa ya ce, "To, madalla." Ya sa wata irin mabusa bakinsa, ya yi ta busa, yana yawo cikin gari rariya rariya. Sai b'erayen nan suka yi ta fitowa ko ta ina, suna binsa tururururu, wad'ansu manya, wad'ansu k'anana, wad'ansu tul-tul, wad'ansu k'yamas-k'yamas. Ga wad'ansu ja wur, wad'ansu fari fat, abin har da shud'd'a da rawaya. Ka ga wad'ansu ruk'u-ruk'u da ciki wad'ansu kuwa ga 'ya'ya k'anana ke biye da su. Sai tsalle-tsalle su ke yi, suna 'yan kuka tsui tsui, kamar suna fara'a da wata bushara.
Da ya kwashe duk, sai ya nufi kogi yana busa, suna biye, mutane na kallo na murna. Da isarsa bakin kogi sai ya fad'a cikin ruwa yana busa, b'eraye kuma ba su san sa'ad da suka bi shi ba, duk suka mutu cikin ruwa, sai d'aya kad'ai ya tsere. Mutane suna yi ta yi wa juna barka. A tsaya ma a fad'i farin cikin da mutanen garin nan su ke yi da rabuwa da wannan bala'i, ya zama k'auyanci.
Da Sarki ya hangi Sarkin Busa na dawowa, sai ya ce wa mutane kowa ya koma gidansa, su kwaba k'asa su lillik'e ramummukan da b'erayen nan suka giggina.
Da Sarkin Busa ya iso, Sarki ya yi masa godiya k'warai. Sarkin Busa ya ce, "To, madalla, sai ka cika alkawarinka ko? Allah ya ba ka nasara."
Sarki ya bata fuska, ya ce a ransa, "To; yanzu in na ba shi sule d'ai d'ai har d'ari, to, ni yaushe zan tara kud'i in ina haka? B'eraye dai ne ganin idon kowa sun mace, ba su ko komowa. In ma ba zarinsa ba d'an tsoho da shi tukuf haka, me zai yi da sule d'ari?"
Ya dubi Sarkin Busa, ya ce, "Ai da wasa na ke yi maka da na ce zan ba ka sule d'ari. Ashe kai ba ka san wasa ba? Ga dai sule sha biyar sun ishe ka. Me za ka yi da kud'i da yawa ga shi ka tsufa?"
Sarkin Busa ya harari Sarki, ya ce, "Zancen banza. Kai d'in ba ka tsufa ba da ka ke alkawari ba ka cikawa? Yi maza ka ba ni in kana ba ni, in ci gaba. Ba a kanku na fara ba!"
Sarki ya ce, "In ba rashin hankalinka ba, yanzu yanzu da isowarka har ka yi aikin sule d'ari? Ko sha biyar d'in da na ce ai don dad'in girmana ne. In an bi k'ididdiga ne, ni ko uku da sisi ba ka ci ba. Dubi fa tun da safe har ta'asar mutum ke aiki a ba shi sisi, balle kai yanzu yanzu! "
Sarkin Busa ya ce, "In fa ba ka ba ni abin da ka yi alkawari ba, yanzu na sake mabusa, ka ga kuma abin da zai faru."
Sarki ya yi fushi, ya ce, "Sake mana! Mu za a ci da burga, sai ka ce ba mutanen birni ba? Wanda ya mutu ban da Allah wa ke iya rayad da shi?"
Sarkin Busa ya ce, "Ko ni ban ce ina iyawa ba, amma ka ga abin da zai faru." Sai ya d'auko wata mabusa ya fara busa, ya shiga gari titi titi yana busawa. Sai yaran gari duk mai iya tafiya, tun daga mai shekara uku har goma, suka yi ta fitowa suna binsa da gudu, suna tafa hannu suna rawa. Wani yaro mai d'an dama daga cikin 'ya'yan Sarki ya rik'a ba da wak'a, saura na amsawa baki d'aya. In ya fad'i ta farko, su kuma su fad'i ta biyu, suna cewa:
Ku zo ga daula wa zai k'i,
Alo alo, mu ci dad'i!
Kowa ya bari ta gota shi,
Alo alo , mu ci dad'i !
Tuwo, nama, sai mun k'oshi,
Alo alo, mu ci dad'i!
Nono da zuma ba mai zari,
Alo alo, mu ci dad'i!
Siliki ran Salla ba datti,
Alo alo , mu ci dad'i !
Zagi, mari, mun huta shi,
Alo alo, mu ci dad'i!
Aikin wahala duk ba ma yi,
Alo alo, mu ci dad'i!
Alo alo, mu ci dad'i!
Alo alo, mu ci dad'i!
Mutane ba su san abin da suka yi da Sarki ba, suna tsammani wasa Sarkin Busa ke yi da 'ya'yansu, sai suka tsaya suna dariya, su ga ikon Allah. Amma da suka ga ya nufi kogi duk sai ransu ya b'aci, suna tsammani zai fad'a ne.
Da Sarkin Busa ya fita bayan gari, sai ya tasam ma wani tsauni nan kusa da gari. Sarki da mutanensa na tsaye na kallonsu. Sarki ya ce a ransa, "Na san dai yaran nan ba su iya hawa wannan tsauni , na ga yadda zai yi da su."
Ko da Sarkin Busa ya isa gindin tsaunin, sai mutane suka ga tsauni ya bud'e. Sarkin Busa ya kutsa ciki, duk yaran nan suka d'uru bayansa. Da suka shige duka, saura d'aya da aka bari can baya yana d'ingishi , sai tsauni ya rufe .
Mutane suka yi ta kuka saboda batan 'ya'yansu. A cikin yaran nan akwai 'ya'yan Sarki su hud'u, su ko ke nan gare shi, duk suka b'ace.
Inda Allah ya kyauta wa Sarki da ya ke mutane ba su san rashin tsaida maganarsa ta sa wannan abu ya faru gare su ba. Da sun sani nan take su ke halaka shi duk da zuriyarsa. To, ga shi kuma duk nasa sun b'ace, balle a ce wani makirci aka k'ulla da shi.
Da uban yaron nan mai d'ingishi ya ga abin da ya faru, sai ya ruga ya jawo d'ansa, yana murna. Aka tambayi yaro me ya sa su ke bin mutumin nan? Yaro ya ce, "Ai mun ji yana cewa mu biyo shi, duk abin dad'i na duniya ya ba mu. Ya ce akwai tabkin zuma, da nono, mu yi ta sha. Ga nama soyayye da dafaffe, wai inda zai nuna mana shinkafa ba a maganarta. Ni yanzu, duk bak'in ciki na ke yi da aka bar ni baya. Yanzu suna can suna cin dad'insu, ni ina nan."
B'eran nan guda kuwa da ya haye, sai ya tafi ya iske wad'ansu b'eraye can, ba irin wad'annan na bala'i ba. Ya rik'a ba su labari, yana cewa, "Ba ku sani ba, na yi d'aron cin dad'i. A can k'etaren rafi wani mai busa ya tara mu zai nuna mana inda daddawa ta ke banza, ga nama. Ga mai, ga mai, ga abinci iri iri, ba mai hana ka ci. Ya ce wajen nan da zai nuna mana ba a tab'a sanin akwai wani abu wai shi kare ba balle kyanwa, k'aramar alhaki. Zan isa, saura kad'an, sai na ji na fad'a cikin ruwa. Yanzu 'yan'uwana na can sun yi k'iba ni rashin sa'a ya sa ni na tabe!"
Saura suka yi ta cewa, "Allah ya sa wata rana mai busan nan ya zo nan k'asar, ya tafi da mu mu ma!"
Sarki ya baza mutane cikin duniya, ko a sami labarin ya b'ulla wani wuri da 'ya'yansu. Aka yi nema, ko labari. Suka gaji suka dangana.
Manyan gari suka ce, "Kai, ba ku sani ba fa, Sarkin nan ke da duk wannan gashin tsiya. Tun da aka halicci duniya kun tab'a ko jin inda irin wad'annan al'amura suka faru?"
Saura suka ce, "A'a, lalle in ba tasam masa muka yi ba, har mu kuma zai sa a halaka mu."
Sai suka taru suka tafi gidan, suka kunna masa wuta. Mai gari ya fito da gudu, suka bi shi da jifa, suka kore shi garin, ya fita tsirara. Iyalinsa kuwa suka fid da su, kowace ta nufi gidansu. Suka kwashe dukiyar da ya tara, da akwatunan kud'i da ya jibge. Suka kona gidan, don kada sabon Sarkin da za su yi ya kwashi ciwon wancan na tsiya.